An kashe wani sufeton ɗan sanda a yayin wani kwanton ɓauna da wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a kwalejin horar da rundunar ’yan sanda (PMFTC) Camp Limankara, Gwoza a Borno.
Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa majiyar Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 0600 a ranar 3 ga Afrilu, 2025, yayin da tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da na makarantar horas da ’yan sanda ta Mopol Gwoza da wasu sassan rundunar ’yan sanda ke sintiri a ƙafa.
- Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi
- APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027
Sufeta Andrawus Musa da ke aiki a rundunar 6PMF a Maiduguri ya samu munanan raunuka yayin harin yayin da maharan suka ƙwace bindigarsa ƙirar AK-47.
Nan take aka wuce da Andrawus zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) amma daga bisani an tabbatar da rasuwarsa da isarsa.
Tuni dai aka ajiye gawar a asibiti domin a tantance ta wadda daga bisani za a yi mata jana’iza.