✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda ku yi amfani da iko cikin adalci — CP Wakili

Ya buƙaci jami’an ’yan sanda da su kasance ƙofar su a buɗe ga jama’a, su saurari ƙorafe-ƙorafensu, tare da gina kyakkyawar alaƙa da su.

Tsohon Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano kuma tsohon Mashawarci na Musamman ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, CP Muhammad Wakili (ritaya), ya jaddada cewa dole ne ’yan sanda su yi amfani da ikon da suke da shi cikin gaskiya da adalci, don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Gombe, a matsayin wani ɓangare na bikin makon ’yan sanda, CP Wakili ya ce ba zai yiwu jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba tare da goyon bayan al’umma ba.

Ya buƙaci jami’an ’yan sanda da su kasance ƙofar su a buɗe ga jama’a, su saurari ƙorafe-ƙorafensu, tare da gina kyakkyawar alaƙa da su.

” ’Yan sanda ba abokan gaba ba ne ga jama’a, su ne ginshiƙin tsaro da ci gaba. Amma dole ne su kula da yadda suke amfani da ikon da aka ba su, domin kada ya rikiɗe ya zama cin zarafi,” in ji Wakili.

Ya yabawa Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Gombe, CP Bello Yahaya, bisa ƙwazon da yake nunawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wakili ya kuma buƙaci al’umma da su bada haɗin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Gombe da ƙasa baki ɗaya.

A nasa jawabin, Kwamishinan ‘Yan sanda na Gombe, CP Bello Yahaya, ya jaddada cewa Ranar ‘Yan Sanda ta Duniya, da ake gudanarwa duk shekara na da nufin tunawa da irin rawar da ’yan sanda ke takawa wajen tabbatar da tsaro.

Ya buƙaci jami’an ’yan sanda da su ƙara ƙaimi wajen kusantar da kansu ga jama’a, su nuna gaskiya da ƙwarewa a ayyukansu, domin gina amana da fahimtar juna.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida na Gombe, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (ritaya), ya jinjinawa CP Yahaya bisa shirya wannan muhimmin taro.

“Wannan irin shiri yana taimakawa wajen gina kyakkyawar fahimta tsakanin jami’an tsaro da jama’a. Ina kira ga rundunar ’yan sanda da su ci gaba da irin waɗannan shirye-shirye,” in ji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa manufar wannan bikin ita ce kusantar da jama’a ga ’yan sanda tare da inganta ayyukansu.