✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin ta’addanci: Nnamdi Kanu ya garzaya kotun daukaka kara

Lauyan Kanu ya ce kotun ba ta hurumin zartar masa da hukunci saboda wasu laifukan a waje aka aikata su.

Shugaban kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu ya garzaya kotun daukaka kara don kalubalantar zarge-zarge bakwai din da ake yi masa masu alaka da ta’addanci.

Ana dai tuhumarsa ne a gaban kotun da Mai Shari’a Binta Nyako da ke Abuja.

Kanu ya kalubalanci hukuncin kotun kamar yadda yake kunshe a cikin hukuncin da aka yanke na karshe na 1, 2, 3, 4, 5, 8 da kuma na 15 na tuhumar da aka yi wa kwaskwarima, wanda aka gabatar a ranar 8 ga Afrilu, 2022.

’Yan jarida sun samu kwafin shari’ar da aka gudanar a Abuja ranar Litinin.

Aminiya ta gano cewar mai shari’a Nyako, ta yi fatali da wasu zarge-zarge takwas daga cikin tuhume-tuhume 15 na cin amanar kasa da Gwamnatin Tarayya ke yi a kan Kanu.

Duk da yin watsi da tuhuma ta 6, 7, 9, 10, 11, 12,13 da 14 da mai shari’ar ta yi, amma ta amince da tuhuma ta 1, 2, 3, 4, 5, 8 da kuma ta 15 da ake yi wa Kanu.

Ragowar tuhume-tuhumen da kotun ta yi watsi da su ya biyo bayan bukatar da Kanu ya shigar na soke dukkan tuhumar da ake masa.

Kanu dai ya shigar da karar ne ta hannun ayarin lauyoyinsa Mike Ozekhome (SAN) da Ifeanyi Ejiofor, a cikin karar da ya shigar a gaban kotun, inda ya ce tuhumar da ake yi masa ta saba da doka.

Ya zargi kotun cewa ba ta da hurumin zartar masa da hukunci kan laifukan da basu dace ba.

Lauyan Kanu, ya shaida wa kotun cewa an tsare wanda ya ke karewa ba bisa ka’ida ba, ana musguna masa da kuma wuce gona da iri daga yayin da ake tsare da shi a Kenya.

Ya kara da cewa tunda wasu daga zarge-zargen da ake yi wa Kanu, an aikata su ne a kasar waje, don haka kotun ba ta da hurumin zartar masa da hukunci.