✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin Rashawa: Manyan Alkalan Najeriya da suka rasa kujerensu

Jerin alkalan Kotun Kolin Najeriya da DSS ta kai samame gidajensu kan zargin rashawa.

Zuwa yanzu a tarihin shari’a a Najeriya, manyan masu shari’a da suka kai mukamin Shugaban Alkalan Najeriya biyu ne suka rasa kujerunsu a bisa zargin rashawa.

Wadannan manyan alkalai kuma shugabannin Kotun Koli ta su ne:

1. Mai Shari’a Muhammad Tanko
2. Mai Shari’a Walter Kanu Ononghen

Kafin saukarsa daga kujerarsa a watan Yunin da muke ciki, Mai shari’a M0hammed Tanko, shi ne Shugaban Alkalan Najeriya kuma mai shugabantar Kotun Koli.

Shi kuma Mai Shari’a Water Ononghen an sauke shi daga irin wannan mukami ne sakamakon zargin shi da ake yi da rashawa a shekarar 2019.

Samamen DSS a gidajen alkalai kan zargin cin hanci: 

A shekarar 2021 jami’an Hukumar DSS sun kai samame gidan Mai Shari’a Mary Odili, matsar tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Peter Odili, a lokacin tana alkali a Kotun Koli.

Kafin nan a shekarar 2016 DSS ta kai samame a gidajen wadandu alkalai a Najeriya da suka hada da.

1. Mai shari’a Sylvester Ngwuta – Alkali a Kotun Koli.
2. John Okoro – Alkali a Kotun Koli.
3. Adeniyi Ademola – Alkali a Babbar Kotun Tarayya.
4. Nnamdi Dimgba – Alkali a babban kotun taraya.
5. Kabiru Auta – Alkali a Jihar Kano.
6. A. I. Umezulike – Babban Mai Shari’a na Jihar Enugu.

Hukumar DSS ta yi kutsen ne a bisa zargin cin hancin da rashawa da ake yi wa alkalan, a inda kuma ta ce ta gano makudan kudade.