Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya maka majalisar dokokin jihar a kotu kan zargin da take masa na karkatar da Naira biliyan 432 a lokacin mulkinsa.
Majalisar dokokin jihar ta zargi gwamnatin El-Rufai ta shekarar takwas (2015-2023) da sace Naira biliyan 432 sannan ta bar wa gwamnati mai ci tari bashi.
A ranar Laraba El-Rufai ya shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta hannun lauyansa, Abdulhakeem Mustapha, inda yake kalubalantar rahoton kwamitin binciken da majalisar ta kafa kan zargin almundahanar.
Karin bayani na tafe