Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouq, ta isa ofishin Hukumar yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) domin amsa tambayoyi kan balakalar Naira biliyan 37.
Ana tuhumar tsohuwar ministan a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ce kan badakalar Naira biliyan 37 da ake zargin wani dan kwangila mai suna James Okwete ya karkata.
A safiyar Litinin Sadiya ta rubuta a shafinta na X cewa, “Ni da kaina na isa hedikwatar EFCC domin amsa gayyatarta ta neman karin haske kan wasu batutuwan hukumar tana bincike.”
Sadiya ta kai kanta oifshin hukumar ne bayan a makon jiya ba ta samu zuwa ofishin domin amasa tambayoyin hukumar game da zargin badakalar ba.
- Badakala: Tinubu ya sa a binciki ministar Jin-kai, Betta Edu
- ’Yan bindiga sun kashe mai gari a Taraba
A makon jiya Sadiya ta bayar da uzurin rashin lafiya a matsayin dalilin rashin amsa gayyatar da EFCC ta yi mata.
Bayanai sun ce tsohuwar ministar, ta nemi EFCC ƙara mata lokaci kan gayyatar titsiye da za a yi mata bisa zargin ta da hannu a badaƙalar Naira biliyan 37 tare da wani dan kwangila, James Okwete.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya ce, tsohuwar ministar ta aiko lauyanta a matsayin wakili tare da neman karin lokaci domin amsa gayyatar, tana mai ba da uzuri na rashin lafiya.
A makon jiya ne, Sadiya Umar Farouq ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta musanta hannu a badaƙalar da ake zargi.
Ta kuma yi iƙirarin cewa kwata-kwata ma ba ta san ɗan kwangilar da rahotanni ke cewa hukumar EFCC ta kama a binciken da take yi dangane da batun ba.