Tsohuwar Minista a Ma’aikatar Jin-ƙai, Sadiya Umar Farouq, za ta bayyana a gaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), bisa zarginta da hannu a badaƙalar fiye da naira biliyan 37 da miliyan 170.
Bayanai sun ce a makon jiya ne hukumar ta aika wa tsohuwar ministar goron gayyata sakamakon wani bincike da ta ƙaddamar a kan aikace-aikacen ma’aikatarta lokacin da take riƙe da muƙamin tsawon shekara shida.
- Tagwayen bama-bamai sun kashe fiye da mutum 100 a Iran
- Mayakan Boko Haram sun kashe mutum 12 a Borno
Ana binciken Sadiya Farouq wadda ta riƙe muƙamin ministar jin-ƙai a gwamnatin Muhammadu Buhari kan zargin hannu a badaƙalar halasta kuɗin haram na fiye da naira biliyan 37 da miliyan 170, da wani ɗan kwangila James Okwete ya aikata.
Wata majiya a EFCC ta shaida wa BBC cewa babu shakka hukumar ta gayyaci tsohuwar ministar amma ba ta yi wani ƙarin haske ba.
A Litinin din makon jiya ce Sadiya Umar Farouq ta fitar da wata sanarwa tana musanta zargin hannu a badaƙalar da ake zargin James Okwete da aikatawa, inda ta jaddada cewa ba ta ma san mutumin da ake magana a kansa ba.
Jaridar Punch ta ce tuni hukumar EFCC ta gayyaci ƙarin jami’ai da suka yi aiki da Sadiya don samun ƙarin haske a kan yadda ma’aikatar ta tafiyar da al’amuranta a cikin shekara shida.
A makon nan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA), Halima Shehu kan zargin almundahana.
Tinubu ya dakatar da ita ne a ranar Talata kan zargin aikata zamba a hukumar, inda ya maye gurbinta da Mista Akindele Egbuwalo a matsayin mukaddashi har zuwa lokacin da za a kammala bincike.