✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mai gari a Taraba

Maharan sun bukaci miliyan daya a matsayin kudin fansa kan kowanne daga cikin mutanen da suka sace.

’Yan bindiga sun kashe mai unguwar kauyen Wuro Musa, Jauro Kabiru Gambo, a Karamar Hukumar Yorro da ke Jihar Taraba.

Aminiya ta ruwaito cewa an gano gawar basaraken ne a dajin da ke kusa da wani dutse a yankin da sanyin safiyar Lahadi.

Wata majiya daga yankin, ta ce an binne marigayi Jauro Gambo a makabartar Jeka Da Fari da ke Jalingo a yammacin Lahadi.

Wannan ya kawo adadin sarakunan gargajiya da ’yan bindiga suka kashe a jihar zuwa hudu.

Maharan sun sace Jauro Gamno ne tare da wasu mutum 17 ciki har da mata bakwai a ranar Juma’a.

Majiyar ta ce sauran mutum 16 din suna hannun ’yan bindigar, inda suka bukaci kudin fansa miliyan daya kan kowane mutum.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya shaida wa wakilinmu cewa DPO din yankin Yorro ya tabbatar da kisan shugaban kauyen Wuro Musa, Malam Kabiru Gambo, da ’yan bindiga suka yi.