Tsohuwar ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farouq ta bayar da uzurin rashin lafiya a matsayin dalilin da ya hana ta amsa gayyatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).
Bayanai sun ce tsohuwar ministar, ta nemi EFCC ƙara mata lokaci kan gayyatar titsiye da za a yi mata bisa zargin ta da hannu a badaƙalar halasta kuɗin haram har naira biliyan 37.1.
- An samu wanda ya fi Dangote kuɗi a Afirka — Forbes
- Dan daba ya kashe limami saboda hana shi shan wiwi a Kano
Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar EFCC na zargin tsohuwar ministar da almundahanar kuɗin da suka haura naira biliyan 37 tare da wani dan kwangila, James Okwete.
Sai dai kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale ya shaida wa Jaridar The Punch cewa, tsohuwar ministar ta aiko musu da lauyanta a matsayin wakili tare da neman karin lokaci domin amsa wannan gayyata, tana mai ba da uzuri na rashin lafiya da take damunta a yanzu.
Jami’an hukumar ta EFCC a jiya Laraba sun yi ta dakon tsohuwar ministar ta zamanin Shugaba Muhammadu Buhari a ofishinsu da ke Abuja, amma suka shafe sa’o’i ba tare da ganin keyarta ba.
A farkon makon jiya ne, Sadiya Umar Farouq ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta musanta hannu a badaƙalar da ake zargi.
Ta kuma yi iƙirarin cewa kwata-kwata ma ba ta san ɗan kwangilar da rahotanni ke cewa hukumar EFCC ta kama a binciken da take yi dangane da batun ba.
Aminiya ta ruwaito cewa a makon jiya ne hukumar ta aika wa tsohuwar ministar goron gayyata sakamakon wani bincike da ta ƙaddamar a kan aikace-aikacen ma’aikatarta lokacin da take riƙe da muƙamin tsawon shekara shida.
A makon nan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA), Halima Shehu kan zargin almundahana.
Tinubu ya dakatar da ita ne a ranar Talata kan zargin aikata zamba a hukumar, inda ya maye gurbinta da Mista Akindele Egbuwalo a matsayin mukaddashi har zuwa lokacin da za a kammala bincike.