✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin Juyin Mulki: DSS ta bayar da belin Fani-Kayode

Fani Kayode ya zargi Atiku da shirya tafka magudi a zaben da ke tafe.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta bayar da belin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode bayan tsare da ta yi a safiyar Litinin.

Aminiya ta ruwaito cewa DSS ta bukaci Fani-Kayode da ya dawo mata da rahoto a ranar Laraba.

Tun a ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar ta gayyaci Mista Femi wanda shi ne daraktan ayyuka na musamman kan sabbin kafafen yada labarai na jam’iyyar APC domin amsa tambayoyi.

Jigon na jam’iyyar APC ya bayyana a ofishin DSS da ke Abuja domin amsa tambayoyi kan zargin da ya yi na wasu manyan janar-janar din soji da wasu ‘yan takarar shugaban kasa ke shirin yin magudi a Zaben 2023 da kuma yunkurin yi wa gwamnati juyin mulki.

Da safiyar yau ta Litinin ce Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya tabbatar da cewa Fani-Kayode ya bayyana a hedikwatar hukumar.

A cikin wata sanarwa da Mista Afunanya ya fitar, ya bayyana cewa tsohon ministan ya kai kansa Ofishin hukumar da misalin karfe 9:00 na safe don amsa gayyatar da aka yi masa.

“Cif Femi Fani-Kayode yana tare da hukumar DSS tun karfe 9 na safe a yau 13 ga watan Fabrairu, 2023 don amsa gayyatar da hukumar ta yi masa,” in ji Afunanya.

Wannan na zuwa ne kimanin kwanaki biyu bayan Fani-Kayode ya yi zargin cewa dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri da wasu janar-janar na soji don shirya manakisar tafka magudi a zaben da ke tafe.

Sai dai Hedikwatar Tsaro ta musanta ganawar da ake zargin ta yi, inda ta yi alkawarin tabbatar da dimokuradiyya a yayin zaben da za a yi kasa da mako biyu.