✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin cikin shege: Kotu tsare mai shekara 65 a kurkuku

Kotu ta tsare wasu tsofaffi a gidan yari bisa zargin yi wa wata karamar yarinya ciki

Kotun Majistare da ke zamanta a Chediya GRA Zariya ta tasa keyar wani tsoho mai shekara 65 wani mai shekara 52 zuwa gidan yari saboda zargin yi wa wata yarinya ciki.

Shi dai mai shekara 65 din, mai gadi ne a wani gidan, shi kuma mai shekara 52 din sana’ar acaba yake yi, sai na ukunsu, kuma dukkansu mazauna garin Tsibiri ne a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Dan sanda Mai gabatar da kara, Sufeto Mannir Nasir, ya shaida wa kotu cewa a ranar 13 ga watan Satumba 2022, wani mai suna Alhaji Nura Yusuf da ke garin Tsibiri ya kai koke zuwa ofishin ’yan sanda da ke Giwa cewar a ranar 1 ga watan Agusta 2022 bayan ya tsananta binciken ’yarsa don sanin wanda ya yi mata ciki sai ta bayyana masa sunayen mutum uku.

Mai gabatar da karar ya sanar da kotu cewa laifin da ake zargin su da aikatawa yana sashi na 368 na Doka Final Kod ta Jihar Kaduna ta shekarar 2017 wadda kuma bai kamata a bayar da su beli ba.

Dukkan wadanda ake zargin ba su musanta tuhumar da ake yi musu a gaban kotu ba.

Mai Shari’a Docas Kitchner ta tsayar da ranar 17 ga watan Oktoba,  2022 domin yanke hukunci kamar yadda mai gabatar da kara ya bukata saboda wadana ake zargin ba su musanta tuhumar da aka yi musu ba.