✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin batanci: Lauyan Abduljabbar ya nemi shaidun masu kara su zama shaidunsu

Lauyna ya kuma roki a sake yi wa Abdujabbar tambayoyi

Lauyan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Barista Dalhatu Shehu Usman, ya nemi Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a jihar Kano da ta dawo da shaidun masu gabatar da kara su je kotu don su zame musu shaidun kariya a shari’ar.

Haka kuma Barista Dalhatu Usman ya yi roko ga kotun zai sake yi wa wanda ake tuhuma tambayoyi.

Sai dai masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Suraj Sa’ida (SAN) sun yi suka game da wadannan roko na wadanda ake kara inda suka ce sake yi wa wanda ake tuhuma tambayoyi da lauyansa yake so ya yi a karo na biyu kawo tsaiko ne ga shari’ar.

Haka kuma, sun ce ba daidai ba ne shaidunsu su zo su bayar da kariya ko goyon baya ga wanda tun da farko suka bayar da shaida akan cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.

Don haka suka nemi kotun ta yi watsi da wannan roko na lauyan kariya.

Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ta amince da bukatar Lauyan Abduljabbar ta sake yi wa Abduljabbar din tambayoyi.

Sai dai ta ce za ta bayyana matsayinta a zama na gaba akan rokon neman yiyuwar dawowar shaidun masu gabatar da kara don su ba wa wanda ake kara kariya a karo na biyu.

Tun da farko kuma, lauyan Abduljabbar Kabara, Barista Dalhatu Usman, ya sake neman kotun da ta mayar da shari’ar zuwa wata kotun ta daban sakamakon zargin da suke yi cewa Alkalin ba zai yi adalci ba la’akari da alakar da ke tsakaminsa da Shaikh Qaribullah Nasiru Kabara, wanda a cewarsa babban makiyi ne ga wanda ake kara.

A kan wannan roko ma, masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Suraj Saida (SAN) sun yi suka game da rokon na lauyan wanda ake kara inda suka kafa hujja da wasu shari’u da suka gudana a manyan kotuna wanda suka nuna cewa ba a canza kotu ba tare da wasu kwararan dalilai ba.

Sai dai Barista Dalhatu ya dage cewar idan har an zargi alkali da rashin adalci to wajibi ne ya mayar da shari’ar wata kotun don tabbatar da adalci domin adalci a shari’a ya fi komai.

Sai dai kotun ta yi watsi da wannan rokon na lauyan Abduljabbar inda Alkalin ya kafa hujja da sashe na 196 (a, b)) na kundin dokar Laifuka ta ACJL ta Jihar Kano (2019) inda ya ce sashen ya nuna ana so wurin da za a yi shari’a ya zama mafi dacewa kuma mafi kusa ga wanda ake kara.

“Idan aka yi la’akari da wannan doka to wannan kotun ta fi kowacce kotu a Kano dacewa da yin wannan shari’a saboda girman matsayinta da kuma kusancinta ga mazauni da kuma gidan gyaran halin da wanda ake kara yake tsare.”

Haka  kuma Alkalin ya shawarci wanda ake kara ya kai korafinsa na rashin adalcin da yake zargin alkalin da shi zuwa gaba.

Daga nan Alkalin ya umarci masu gabatar da kara da su ci gaba da yin tambayoyinsu ga wanda ake kara a matsayinsa na shaidar kariya na farko.

Bayan kammala tambayoyin ne Kotun ta dage zaman sauraren shariar zuwa ranar 11 ga watan Agusta, 2022.

Gwamnatin Jihar Kano ce dai ta gurfanar da Abduljabbar Kabara gaban kotun bisa zargin sa da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kuma tayar da hankulan jama’a.