Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofor Kudu a Kano ta ba da umarnin damka kaset din karatuttukan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ga masu gabatar da kara don yin nazari a kai.
Tunda farko a zaman na ranar Alhami, kotun karkashin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ta yi umarni da kunna kaset din karatuttukan don sauraro a gabanta, kamar yadda lauyoyinsa suka nema.
- ‘Tinubu ya yi wa Gwamnonin APC alkawarin Mataimakin Shugaban Kasa’
- ISWAP ce ta kai hari a cocin Ondo – Gwamnatin Tarayya
Ana dai zargin Abduljabbar Kabara da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) a cikin karatuttukan da ya yi a wasu lokuta a baya.
Idan za a iya tunawa, tun a ranar 31 ga watan Maris na 2022 lauyoyin Abduljabbar suka gabatar wa kotun da kaset din (memory) da ya kunshi karatuttukan wanda suke karewa.
Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce a iya fahimtarsa na cewa sai a hukuncin karshe ne za a kunna memory din bai yi kama da adalci ba.
“A fahimtata, ana tuhumar wanda ake kara ne da yin wasu kalamai na batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam cikin karatunsa da yake yi. Zargin da ya musanta aikatawa, har ma yake da’awar cewa shi korewa yake yi. Don haka tsantsar adalci shi ne a kunna karatun don kotu ta saurara.”
A cewarsa, bai gamsu da sukar da lauyan gwamnati ya yi na nuna rashin ingancin shaidar (Certificate) din ba, don haka ya ce ya karbi wannan kaset domin a kunna a saurara.
Lauyan wanda ake kara, Barista Dalhatu Shehu Usman ya shaida wa kotun cewa duk da yake yau [Alamis] ya fara shigowa cikin karar, a shirye yake ya ci gaba da shariar.
Haka kuma ya bayyana cewa ba shi da wani roko da zai yi.
Shi ma dai lauyan gwamnati, Usman Muhammad, ya ce ba za su ce komai akan hakan ba don haka sun yi biyayya ga kotun.
Daga nan ne aka kunna memory domin jin kalaman da ake zargin malami da yi a cikin karatunsa.
Bayan sauraren karatun na tsawon lokaci masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Usman Muhammad sun nemi kotu ta ba su kaset din don su yi nazarinsa da kyau.
Da yake tattaunawa da manema labarai, jagoran masu gabatar da kara Barista Usman Muhammad ya ce sun yi suka game da ingancin kaset din inda suka ce a fahimtarsu “hade-hade ne kawai aka yi na dabaru domin idan an saurara za a ji wani bangaren karatu ne, wani bangaren kuma mukabala ce, wani bangaren kuma karatun Dokta Gumi ne. Muna nan za mu kawo namu kaset din wanda yake hannun yanwsanda bayan da kwararru suka tantance ingancinsa.”
Shi ma a tasa tattaunawar, sabon lauyan Abduljabbar Kabara wato Barista Dalhatu Shehu Usman ya ce daga sauraren kaset din za a san cewa wanda yake karewa bai aikata abin da ake zarginsa da shi ba, sai ma kokarin kore batancin daga janibin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Daga nan ne kotun ta dage zaman shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2022.