Hedikwatar ’yan sandan Nijeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II domin amsa tambayoyi kan wani lamari da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano.
A baya dai rundunar ’yan sanda tare da sauran wasu jami’an tsaro a jihar sun soke duk wani hawan bikin Sallah, musamman jerin gwanon dawakai a jihar, saboda dalilan tsaro.
- Motar fasinja ta kama wuta wasu sun tsallake rijiya da baya
- Rashin tsaro a Filato ya wuce rikicin manoma da makiyaya – Muftwang
Sai dai a yayin da Sarkin ke tattaki domin halartar Sallah a filin Idi na Ƙofar Mata a ranar 30 ga watan Maris, an caka wa wani ɗan banga da ke kare Sarkin wuƙa har lahira, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Bayan faruwar lamarin, wasu sun shaida wa majiyar Daily Nigerian cewa tun da farko babban Sufeton ’yan sandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya umarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya kama sarkin.
Kamar yadda aka samu rahoto, Kwamishinan ya bayyanawa Sufeto Janar ɗin cewa, lamarin ba shi da alaƙa da keta dokar hana hawan Sallah, kuma Sarkin bai yi amfani da dawakai wajen ziyartar gidan gwamnati ba kamar yadda al’adar ta tanada.
Sufeta Janar ya umurci sashen leƙen asiri na rundunar da ta karbe fayil ɗin ƙarar tare da gayyatar Sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.
A wata wasiƙar gayyata da ya sanya wa hannu Kwamishina ’yan sanda CP Olajide Ibitoye, sun gayyaci sarkin da ya gurfana a gaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar a ranar Talata 8 ga Afrilu da ƙarfe 10 na safe.