Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano, ta fara sauraron shaidun kariya a shari’ar da take yi wa fitaccen Malamin nan na addinin Islama, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Ana dai zargin Abduljabbar Kabara da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma tayar da hankalin jama’a.
Bayan wanda ake zargi ya gurfana a gaban kotun Alkalin Kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya nemi da ya zabi daya ko rantsuwa ko alkawari cewa zai fadi gaskiya game da shaidar da zai bayar inda wanda ake zargin ya ce rantsuwa zai yi da Alkur’ani mai girma.
Hakan ce ta sanya Alkalin ya umarci magatakaddar kotun, Ibrahim Faruku da ya rantsar da shi.
Bayan ya kammala rantsuwar ne sai lauyansa A.O.Muhammad (SAN) ya karanto masa kunshin tuhume-tuhume har guda 4 da masu gabatar da kara suke zarginsa game da kalmomi na batanci da ya yi ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).
Sai dai Abduljabbar ya musanta su gaba daya inda ya ce shi kokarin kore kalmomin yake yi daga janibin Annabi Muhammad (SAW).
Daga nan ne sai ya fara kare kansa game da tuhume-tuhume guda 2 da suka hada da lafuzzan fyade da kwace da ya danganta su ga Annabi Muhammad (SAW) a sha’anin aurensa da Nana Safiya.
Lafuzzan da masu gabatar da kara suka ce babu su a cikin dukkanin Hadisan da Abduljabbar din ya bayar da su a matsayin madogara inda suka ce shi ya kirkire su don yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
A kan haka ne Abduljabbar din ya ce ya fadi wadancan kalmomi ne bisa ma’anar da suka zo a cikin Hadisan ba wai a lafuzzan da masu gabatar da kara ke cewa ba su gani a cikin Hadisan ba.
A lokacin wannan kariya, Abdujabbar Kabara ya gabatar wa kotu tare da karanta wasu littattafai guda 16 a matsayin hujjojin da ya yi dogaro da su.
Lauyan Abduljabbar ya roki kotun da ta ba su wata rana domin a dawo a ci gaba da kariya game da sauran tuhume-tuhumen guda biyu da ake yi wa wanda ake zargi.
Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya tambayi jagoran masu gabatar da kara kuma lauyan gwamnati, Barista Saida Suraj (SAN) ko zai ce wani abu game da rokon lauyan wanda ake zargi, a nan ne Lauyan Gwamnatin ya bayyana wa kotu cewa ba shi da suka akan rokon da lauyan Abduljabbar din ya yi.
Alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya umarci lauyan Abduljabbar A.O Muhammad (SAN) ya ba wa kotun dukkanin littattafan da Abduljabbar ya gabatar da su a matsayin hujjojinsa da kuma umarnin a yi kwafinsu a ba wa lauyoyin gwamnati.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, bayan haka ne kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar Alhamis, 17 ga watan Maris na 2022.