✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zango da Naziru a albam din ‘Kukan Kurciya’

Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa Adam A Zangon ya kammala daukar albam din wakokinsa mai suna ‘Kukan Kurciya’ a Kaduna a jiya Alhamis.Kamfanin White…

Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa Adam A Zangon ya kammala daukar albam din wakokinsa mai suna ‘Kukan Kurciya’ a Kaduna a jiya Alhamis.
Kamfanin White House da ke  karkashin kamfanin Prince Zango Nigeria Limited ne ya dauki nauyin albam din, inda kuma Adam A Zango ya ba da umarni.
Albam din ya kunshi wakoki da dama, inda ya rika yin wakokin da sauran mawakan Hausa wadanda suka hada da Naziru M Ahmad da Nura M Inuwa da Umar M Shariff da sauransu.