✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar tsadar rayuwa ta barke a Legas

Zanga-zangar tsadar rayuwar ta barke ne kasa da awa 24 da Kungiyar Kwadago ta Najeriya za ta fara nata a fadin kasar.

Jama’a sun fara zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya a Jihar Legas.

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam mai suna ‘Take It Back Movement’ ce ta kaddamar da zanga-zangar, duk da hanawar da kwamishinan ’yan sandan jihar, Adegoke Fayoade, ya yi.

Zanga-zangar tsadar rayuwar ta barke ne kasa da awa 24 da Kungiyar Kwadago ta Najeriya za ta fara nata a fadin kasar.