Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta lashi takobin fara zanga-zanga da yajin aiki a makon gobe kan karin farashin wutar lantarki da man fetur da gwamnati ta yi.
Shugaban NLC na kasa, Ayuba Wabba ya ce babu wani lallashi da zai sa kungiyar janye yajin aikin sai dai idan gwamnati ce ta janye kare-karen farashin.
Bayan kammala taron Kwamitin Zartarwar kungiyar ta kasa a ranar Litinin, Wabba ya ce shugabannin kungiyar a jihohi 36 sun yi ittiffaki janye batun dakatarwar da yayin aiki da zangz-zangar da shirya gudanarwar a baya.
A baya gwamantin tarayya ta bukaci tattaunawa da kungiyoyin kwadago domin kauce wa yajin aikin da suka shirya shiga saboda kare-karen farashi.
- Mutane na wa gwamnoni kallon barayi —El-Rufai
- Garkuwa: An ceto jami’an FRSC 26 a Nasarawa
- Abin da ya kamata ku sani kan shirin tallafin gwamnati na Survival Funds
Sai dai zaman bai yiwu ba, saboda gajartan sanawar, wanda ya sa aka Ministan Kwadago, Chris Ngige dage zaman zuwa ranar Talata.
Sai dai ana ganin sabon matsayin na NLC martani ne ga wata kungiya mai goyon bayan gwamnati da ta gudanar da gangamin goyon bayan kare-karen farashin da cewa an yi ne domin amfanin ’yan Najeriya.
A lokacin ganagamin, Shugaban kungiyar ta (NPM) mai goyon bayan gwamnatin, Okpokwu Ogenyi, ya ce kare-karen za su amfani ’yan Najeriya amma za su cutar da masu sace dukiyar kasa da suna tallafin mai ko “ayyukan wutar lantarki marasa yiwuwa” tun 1999.
“Muna kira ga NLC, TUC da sauran manyan ’yan Najeriya da su daina yi wa gwamnati baranza a kan kyawawan manufofinta.
“Masu sukar gwamnati a kan cire tallafin mai suna yi ne don biyan bukatunsu ba don amfnin al’umma ba; me zai sa ’yan kwadago su yi barazanar shiga yajin aiki?” inji shi.