Kungiyar Matasa ta Arewa Maso Gabar ta bukaci matasa musamman masu zanga-zangar EndSARS a wasu yankunan kasar nan da su kai zuciya nesa tare da yin Allah wadai da asarar rayuka da ta dukiya da lamarin ya haifar.
Jagoran kungiyar, Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham ne ya gabatar da rokon jim kadan bayan wani zama da su ka yi a kan lamarin a Birnin Abuja, a ranar Alhamis.
- Diyar Ganduje ta caccaki gwamnati kan zanga-zangar #EndSARS
- Arewa ake neman karyawa da zanga-zangar #EndSARS -Sheik Jingir
- Kungiyoyin arewa sun janye zanga-zanga saboda rikici
Abdurrahman Kwaccham, ya bayyana juyayin kungiyar a kan abubuwan da su ka faru musamman a jihohin Edo da Lagos da kuma yankin Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma jihar Ribas, inda ya ce yanayin salon da zanga-zangar ta koma abin takaici ne da tada hankali.
Ya ce magance abinda ke faruwa na bukatar hadin kai daga dukkan bangarori, tare da mantawa da banbancen siyasa da na yanki ko addini, inji shi.
“Dole ne jagororin al’umma a duk inda su ka samu kansu na matakin shugabanci, su fito su ja hankalin matasan nan kan su janye.
“Za a iya ganin farkon fitina amma ba wanda yasan inda za ta kai da kuma lokacin da za ta kare.
“Tsagerun da su ka karbe ragamar zanga-zangar zuwa matakin kone-kone da kwasar ganima, ba lallai ba ne su na da masaniya a kan yadda hakan ta kai kasashe irin su Somaliya da Venezuela da ma Sudan a baya-bayan nan.
“Da farko mun yi tsammanin za su kara bukatu irin na magance matsalar tsaro a jihohin arewa musamman irinsu Katsina da Zamfara da sauransu, da kuma matsalar da ta jima ta Boko Haram, amma sai mu ka ji sun sako wasu karim bukatu na daban.
“Wannan ba daidai ba ne, a saboda haka mu na kira garesu da su dakata hakanan,” inji Kwaccham.