Ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta ce zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin yin zanga-zanga ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin ƙasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan ƙasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya.
Rundunar ta ce zanga-zangar da wata ƙungiya mai suna “Take It Back” ta shirya tana zuwa ne a lokacin da bai dace a yi zanga-zanga a ƙasar ba.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce rundunar ba ta adawa da ‘yancin ‘yan ƙasar na taruwa da yin gangami da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su.
Sai dai kuma sanarwar ta ce rundunar na fargaba game da burin waɗanda suka shirya yin zanga-zangar rana ɗaya da ranar da aka ware domin yaba wa irin jajircewa da sadaukar da kai na ‘yan sandan Nijeriya.
“Bisa ga ingatattun ɗabi’un da ƙasashen duniya ke bi wajen yabawa da nasarorin ‘yan sandansu, gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sandan Nijeriya,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa bikin zai samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar daga fannoni daban-daban, ciki har da sufeto janar na ‘yan sandan ƙasashen ƙetare da kuma jami’an diflomasiyya.
“Dalilin gudanar da zanga-zanga a irin wannan ranar abin dubawa ne kuma a iya cewa wani mataki ne na ɓata sunan ‘yan sandan Nijeriya da ƙasar ma baki ɗaya,” in ji sanarwar.
“Saboda haka rundunar ‘yan sandan Nijeriya tana bai wa waɗanda suka shirya wannan zanga-zangar shawarar janyeta saboda lokacin bai dace da ita ba kuma tana da manufar aikata ɓarna,” in ji Olumuyiwa.
Dalilin da za mu yi zanga-zanga — Take It Back
Sai dai duk da wannan gargaɗi, ƙungiyar ta Take It Back ta ce tana nan kan bakarta domin nuna adawa kan abin da ta kira mulkin kama karya da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi a ƙasar nan.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ƙarshen mako, jagoran ƙungiyar, Juwon Sanyaolu, ta ce za su gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar domin nuna adawa rashin shugabanci nagari da kuma daƙile ’yancin faɗar albarkacin baki.
Sanyaolu ya buƙaci masu zanga-zangar a Jihar Legas da su haɗa dandazo a ƙarƙashin Gadar Ikeja.
Ya ce waɗanda ke Jihar Oyo za su haɗu ne a kan titin Iwo a Ibadan; yayin da zanga-zangar za ta tashi ne a filin shakatawa na Isaac Boro da ke Fatakwal a Jihar Ribas.