Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta sanar da cafke mutum 873 da ake zargi da hannu a lalata dukiyoyin gwamnati da na jama’a yayin zanga-zangar yunwa da aka gudanar a jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Salman-Dogo Garba ne, ya bayyana hakan yayin da ya gabatar da waɗanda ake zargi a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Litinin.
- Babu wanda aka kashe a zanga-zangar yunwa a Kano —’Yan sanda
- ICPC ta tsare manyan jami’an NAHCON a ofis kan badakalar N90bn
Ya ce, “Bayan abin da ya faru, mun kama mutum 873 kuma mun ƙwato kayan da aka sace da dama.
“An gurfanar da mutum 600 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da haɗin baki, tunzura jama’a wajen tayar da hankali, sata, ɓarna da kuma ƙone gine-gine.
“Mun kuma kama mutum 150 da suka karya dokar hana fita da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa.
“Haka kuma, mutum shida da ake zargi da jagorantar lalata da kuma ƙone Kamfanin Buga Takardun Kano (KPP) sun shiga hannu.
“Bugu da ƙari, mun miƙa mutum 76 waɗanda aka kama ɗauke da tutar Rasha, zuwa babbar hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja domin ci gaba da bincike kan zargin tayar da hankali.”
’Yan sanda sun kuma kama mutum 41 da ake zargi da aikata manyan laifuka da suka shafi fashi da makami, garkuwa da mutane, da satar motoci.
Kazalika, sun ƙwato bindigogi guda biyu ƙirar AK-47 da wasu kayayyakin da aka sace a sakatariyar Audu Baku, Ofishin Cibiyar NCC da wasu manyan kantuna a jihar.
Garba, ya ce duk da ƙalubalen da rundunar ta fuskanta yayin zanga-zangar, amma ta samu nasarar kama wasu ’yan bindiga guda biyu, ’yan fashi da makami guda biyar, ɓarayin mota guda takwas, masu fataucin mutane guda biyu, wani mai safarar miyagun ƙwayoyi, da kuma ‘yan daba guda 23.
’Yan sanda sun kuma ceto wasu mutum 13 da aka yi fataucinsu kuma sun ƙwato bindigogi guda biyu kirar AK-47 da alburusai 47.
Har wa yau, ya ce sun ƙwato motoci guda takwas, da kuma buhu huɗu na ƙwayar Exol.
Sauran kayayyakin da suka ƙwato sun haɗa da babura guda biyu, shanu 22, tumaki 15 da kuma jakuna guda huɗu.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda tare da hana aikata laifuka, da kuma kare haƙƙin ‘yan ƙasa na yin zanga-zangar lumana.