✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zanga ta barke a Majalisa kan Harin Mauludin Kaduna

Masu zanga-zanga a Majalisa kan kisan Masu Mauludin Kaduna sun nemi Ministan Tsaroya magance matsalar tsaro ko ya ajiya aikinsa.

’Yan Najeriya sun yi wa Majalisar Dokoki ta Kasa cikar kwari, suna zanga-zanga kan kisan Musulmi kimanin 90 da jirgin soji ya yi a wurin taron Mauludi a Jihar Kaduna.

Masu zanga-zangar sun bukaci Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da ya magance matsalar tsaro da ke addabar Najeriya ko kuma ya ajiya aikinsa.

“Tun da ministan tsaron nan ya kama aiki matsalar tsaron Najeriya sai kara tabarbarewa take,”, in ji jagoran zanga-zangar, karkashin inuwawr Majalisar Matasan Najeriya (NYCN), Nasir Ishaku.

“Sai rasa sojoji da ’yan sandan Najeriya ake ta yi. Ga daliban jami’o’inmu a hannun yan bindiga, babu wanda ya san inda suke.

“Wadanndan kadai sun isa zama shaida kan rashin kwarewar ministan tsaron yanzu. Saboda haka ya farka daga barcinsa ko kuma ya ajiye mukaminsa.”

Ishaku wanda kuma shi ne shugaban kungiyar matasan Arewa, ya ce yaza wajibi a bi wa wadanda aka kashe a harin hakkinsu.

Ya ce yadda ake kashe mutane kullu-yaumin musamman a Arewa, abin da ba za a lamunta ba ne.

Don haka ya bukaci a gudanar da cikakken bincike kan harin na ranar Lahadi domin daukar tsattsauran matakin da ya dace.