Akalla mutum 164 ne aka kashe cikin mako daya a zanga-zanga a kasar Kazakhstan, kamar yadda Ma’aikatar Lafiyar kasar ta shaida wa manema labarai.
Kazalika, sama da mutum 2,200 ne suka ji rauni a yayin nuna adawa ga gwamnatin kasar a lokacin zanga-zangar.
- Sanya Takunkumi: Sojojin Mali sun yi fito-na-fito da kungiyar ECOWAS
- Kar a yi la’akari da jam’iyya ko addini a Zaben 2023 —Sanusi II
A cewar ma’aikatar lafiyar, an duba mutum 719 da suka jikkata a ranar Lahadi, yayin da mutum 83 ke cikin mawuyacin hali.
Sai dai har yanzu mahukuntan gwamnatin kasar sun gaza tofa albarkacin bakinsu kan yadda zanga-zangar ke ci gaba da tsamari.
Zanga-zangar ta fara ne tun satin da ya gabata, inda dubban mutanen kasar ke nuna adawa ga hukuncin gwamnatin na kara farashin man fetur da ta yi.
Zanga-zangar ta jawo koma baya da kuma durkeshewar kasuwancin mutane da dama a kasar.
Sai dai rahoton wani gidan talabijin ya bayyana cewar a iya yankin Almaty, mutum 103 ne suka mutu, ciki har da kananan yara.
Amma baya-bayan nan hukumomi a kasar sun ce mutum 40 ne suka rasa rayukansu ciki har da jami’an soji da na ’yan sanda.
Sanarwa daga Fadar Shugaban Kasar, Kassym-Jomart Tokaye, ta ce gwamnatin na kokarin shawo kan zanga-zangar cikin lumana don kaucewa tashin-tashina da fada wa mummunan yanayi.