‘Yan Sanda a Amurka sun umarci a gaggauta kwashe muhimman kayayyakin dake ginin Majalisar kasar yayin da masu zanga-zanga magoya bayan Shugaba Donald Trump suka balle shingen da aka saka a kokarinsu na kutsa kai ciki.
Tuni dai ‘Yan Sandan suka umarci ma’aikatan majalisar da su kauracewa wurin, bayan Trump ya umarci magoya bayansa da kada su bari a ba Joe Biden takardar shaidar lashe zaben kasar.
- Yanzu zaben Amurka ya fi na kasashe masu tasowa lalacewa – Trump
- Sarakuna ke gayyato ’yan bingida —Gwamnan Neja
“Yanzun nan na kubutar da ofishi na daga barazanar masu zanga-zangar. Yanzu haka ga su nan suna ta’asa da cin zarafin ‘yan sandan ginin,” inji ‘Yar Majalisa Nancy Mace a wani sako a shafinta na Twitter.
“Wannan ba daidai ba ne. Hakan bai dace da mu ba. Ina matukar takaici da halin da kasarmu ke ciki a halin yanzu,” inji ta.
Dubban masu zanga-zangar ne dai ke rera wakokin nuna goyon baya ga Trump a da’awarsa ta tafka magudi a zaben kasar yayin wani gangami a kusa da Fadar White House ranar Laraba.
Suna dai kokarin ganin ba a ba zababben Shugaba Joe Biden takardar shaidar lashe zabe ba ne wanda aka tsara yi a wurin.
“Ba za mu taba kyalewa a rufe mana baki ba,” Trump yake shaidawa magoya bayansa wadanda suka taru domin sauraron jawabinsa.
Kazalika, magoya bayan nasa sun yi ta shewa lokacin da ya ce sai sun dakatar da abinda ya kira da sata kiri-kiri.
Rahotanni dai sun ce ya zuwa yanzu an cafke masu zanga-zangar har mutum shida bisa zargin su da cin zarafin ‘yan sada.
To sai dai a wani mataki mai kama da raba-gari, Mataimakin Shugaba Trump, Mike Pence ya ki yarda ya bayar da kai bori ya hau wajen ganin ba kawo tsaiko a lamarin.
Mike dai ya mayar wa da Trump martani inda ya ce ba shi da hurumin kawo tarnaki ko canza abinda Amurkawa suka zaba.