Rundunar tsaro ta sibil difens reshen Jihar Kano ta gargadi masu sana’ar gwangwan da su guji sayen kayayyakin da wasu batagari suka sato a yayin gudanar da zanga zanga a ranar Alhamis din da ta gabata.
Kwamandan Rundunar Muhammad Lawal Falala ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da mutane 108 da suka kama a hedikwatarsu da ke Kano.
- An sassauta dokar hana fita a kananan hukumomi 3 a Yobe
- Ba zan dawo da tallafin man fetur ba — Tinubu
Falala ya bayyana cewa sun kama mutanen ne da ake zargi da lalata gine-ginen gwamnati da kuma sace kayayyaki masu daraja a wurare daban-daban a lokacin da a yayin gudanar da zanga zangar tsadar rayuwa da ta rikide ta koma tarzoma.
Da yake karin haske, Kwamanda Falala ya bayyana cewa jami’ansu da ke bangaren yaki da barnata dukiyar gwamnati ne suka kama batagarin.
Ya bayyana cewa wadanda aka kama ana zargin sun gudanar da aika-aikar ce a ofishin Hukumar Sadarwa ta Kasa da ake gab da bude shi da kuma madaba’ar gwamnatin jihar inda suka wawushe kayayyakin da ke ciki.
A cewar rundunar, ta kuma kama wasu mutanen a unguwar Sabon Gari da Fagge da sauransu.
Da yake yi wa manema labarai jawabi, Falala ya ce “wadannan su ne ire iren kayayyakin da suka lalata da suka hada da karafan da suka raba tsakanin tituna biyu.
“Ga kuma wasu kayayyaki daban-daban da suka hada da kwamfuta da talabijin da durowoyi da gilasan tagogi da kujerun da sauransu.”
A cewarsa an samu kayayyakin ne yayin da wadanda ake zargin suka je kwashe kayayyakin a wurin da suka boye su a ginin Sakatariyar Audu Bako bayan tsohuwar tashar Kano Line.
Har ila yau, Falala ya ce jami’ansu sun yi nasarar gano wani injin janareta samfurin Kamfanin Mikano Mai karfin 59KVA wanda ke ba fitilun titin Dorayi wuta.
“Sai dai yayin da wadanda suka dauko janaretan suka hangi jami’anmu sai suka jefar da shi suka gudu.”
Kwamandan ya bayyana cewa rundunarsu ta fara gudanar da bincike kan lamarin da zarar sun kammala za su gurfanar da su gaban kuliya.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su ja wa ’ya’yansu kunne da su guji aikata abubuwan assha saboda rundunar ba za ta sanya idanu ta bari a ci gaba da barnata dukiyar gwamnati da ta al’umma ba.
“Za mu ci gaba da kare gine-gine da dukiyar gwamnati da kuma na al’umma,” inji shi.