Iyayen wasu matasa da aka tura gidan yari kan zanga-zangar yunwa a Jihar Kaduna, sun bayyana cewa ’ya’yan nasu ba su fita zanga-zangar ba, amma jami’an tsaro suka shiga har cikin gida suka kama su suka tafi da su.
Duk da umarnin kotu da Shugaban Kasa Bola Tinubu da kotu na sakin matasan, iyayen wadannan matasa sun ce ba a sallami nasu ’ya’yan ba, sai ranar Larabar nan.
Hakan na zuwa ne bayan kotu a Abuja ta sallami matasan da aka gurfanar a gabanta bayan Gwamnatin Tarayya ta janye zargin cin amanar kasa da yunkurin juyin mulki a lokacin zanga-zangar na watan Agusta.
Amma Malam Shu’aibu, wanda aka fi sani da Baban Jibril, mazaunin garin Kaduna, ya ce, har cikin gidansa jami’an tsaro suka shigo a cikin dare suka kama dansa Jibril, aka kai shi kotu sau daya, daga nan aka kai shi Gidan Yarin Kaduna.
- ‘A haramta wa baki zuwa Borno karatun allo’
- Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda
Dattijon, wanda a cewarsa, Jibril bai shiga zanga-zangar ba, ya bayyana cewa, daga lokacin “Sai dai mu je mu kai masa ziyara domin ba mu da kudin da za mu yi belin sa.
“A yanzu taimakon Allah nake neman Ya sa gwamnati ta sake shi domin shi ba a kai shi Abuja ba,” in ji shi.
Malam Shuaibu ya yi wannan korafi ne bayan a ranar 5 ga watan nan na Nuwamba, 2024, an saki wadanda aka tsare a gidan yarin Kuje da ke Abuja, bayan gwamnati ta janye zargin da take musu.
A ranar 1 ga watan Agusta aka fara zanga-zangar wadda ta karade Nijeriya, domin nuna adawa da yunwa da tsadar rayuwa da suka addai al’ummar kasar tun bayan janye tallafin mai da sauran matakan gwamnati da suka biyo baya.
Akalla matasa 12 ’yan unguwar Rigasa da ke tsare a gidan Yarin Kaduna tun bayan kama su da aka yi a lokacin zanga-zangar yunwar ne suka shaki iskar yanci kwanaki takwas bayan sakin sauran masu zanga-zangar a Abuja.
Aminiya ta gano cewa wadannan matasa, sai ranar Larabar nan aka bayar da belinsu, kuma ba sa cikin sama da 70 da shugaban kasa ya ba da umurnin sakin su a Abuja.
Su wadannan matasa 12 bincike ya nuna dukkansu ’yan unguwar Rigasa ne Kaduna, kuma tun da aka kai su kotu bayan kama su kimanin watanni uku da suka wuce, ake tsare da su a gidan Yari inda suke a tsare a cewar iyayansu.
Malam Shu’aibu, wanda aka fi sani da Baban Jibril, mazaunin unguwar Rigasa a Karamar Hukumar Igabi, ya ce an kama dan nasa an tsare shi a gidan Yari na Kaduna tun bayan kama shi da aka yi a watan Augusta.
“Ko a makon nan da ya gabata na ziyarce shi na kai masa kayan abinci da magani domin ba shi da lafiya. Shi ne ma yake fada min cewa su kusan 12 ne ke a tsare.
“Na ga wasu daga cikinsu kuma ni na rasa yadda za a yi ko wajen wanda zan je domin a taimaka min a sako shi domin bai shiga zanga-zangar da aka yi ba, saboda ina gida a ranar inda na kuma hana yarana fita, Amma kwatsan sai jamitan tsaro suka shigo cikin gida suka kama min yaro,” inji shi.
Ya ce sun sami zuwa wajen wani lauya da ya taimaka masu har ta kai ga an kai yaran kotu har suka sami belinsu a ranar Larabar nan.
“Gaskiya mun ji dadin bayar da belin su a kotu, mun gode da bibiya da taimako da aka nuna mana,” in ji shi.
Shi ma Abubakar Dattijo, dan uwa daya daga cikin wadanda ake tsare da su, mai suna Ahmad Aliyu, ya ce suna nan suna ta kokarin ganin an sako yaron.
Ya ce, Ahmad, “Yaro ne da ke sana’ar tela kuma kwanan nan ya kammala karatunsa na sakandire domin samun shiga aikin soja sai kwasan jami’an suka shigo gidansu da misalin uku na dare aka kama shi.
“Kuma tun da aka kama shi aka wuce da su wajen ’yan sanda daga nan aka kai su kotu sai gidan yari.
“Mu dai ba mu da kudin da za mu bayar domin wai ana zargin su da cin amanar kasa sannan kuma wai sai an biya wasu kayayyaki da aka farfasa.
“Shi kuma Ahmad ba a lokacin zanga-zangar ma aka kama shi ba, sai bayan kusan sati biyu da faruwar lamarin,” in ji shi.
Shi ma ya nuna farin cikinsa dangane da bayar da belin dan uwan nasa da aka yi watanni bayan kama su.
Shi ma Abubakar Aliyu kawun Kabiru Abdullahi, daya daga cikin wadanda ke tsare a gidan yari, wanda shi aka kama bayan zanga-zangar da ta gudana a yankin Rigasa.
“Kabiru yaron yayata ne kuma shi Keke NAPEP yake tukawa, sannan shi bai shiga zanga-zangar ba amma daya daga cikin yaran da yake bai wa kekensa ne ake zargin wai ya shiga zanga-zangar amma ba Kabiru ba.”
Ya kara da cewa sun bukaci a karbi bilinsa amma kudin da aka bukata a hannunsu da yawa kuma ba su da wannan kudi, don haka suke neman gwamnati ta taimaka ta kuma tausaya kamar yadda ta tausayawa sauran Yan zanga zanga-zangar da aka Saka mako daya da ya gabata.