✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

So muke EFCC ta ci gaba da binciken Badakalar Matawalle a Zamfara —Matasa

Suna neman a dauko fayil din binciken karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, a lokacin da yake gwmanan Zamfara

Dandazon wasu matasa sun mamaye hedikwatar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta Kasa (EFCC) da ke Abuja ranar Laraba domin neman hukumar ta dakko kundin binciken tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle na zargin cin hanci da rashawa. 

tsohon Gwamnan Zamfara Matawalle shi ne karamin Ministan tsaro a halin yanzu.

Shugaban matasan, a karkashin kungiyar Tinubu Youth and Women Network, Kwamared Aliyu Yunusa, ya ce jinkirin yin shari’ar duk da alkawarin da EFCC ta yi, na jefa waswasi a zukatan ’yan Najeriya danagane da hukumar.

“Muna taimaka wa gwamnati wurin gano matsalolin cin hanci da hanyoyin magance su cikin sauki domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.

“Mun himmatu wurin ba da gudunmawa don kawar da ayyukan cin hanci ta hanyar ganin an hukunta wadanda suka aikata.

“A matsayinmu na masu biyayya ga jam’iyyar APC, muna son EFCC ta binciki lamarin ta kuma hukunta wadanda ke da hannu wurin karkatar da kudaden jama’a.

“Hakan zai zama izina ga wasu idan aka yi la’akari da yadda rashawa ke zama ruwan dare a ma’aikatun gwamnati, kamar abin da ya faru da ministan agaji.”

Shugaban masu zanga-zangar ya ce tun a ranar 18 ga Mayu, 2023, kakakin EFCC na wancan lokacin, Osita Nwajah, ya bayyana cewa Matawalle na fuskantar bincike kan zargin almundahana, kwangilar bogi da kuma karkatar da sama da N70bn.

“Binciken da hukumar ta gudanar ya zuwa yanzu ya nuna sama da kamfanoni 100 ne suka karbi kudade daga cikin kudaden jama’ar Zmafara, ba tare da wata shaida ta aikin da aka yi wa jihar ba.

“Wasu daga cikin ’yan kwangilar da hukumar ta gayyace su sun bayyana mamakin su kan yadda ake zargin su da laifin, domin kuwa a cewarsu, tsohon gwamnan jihar ne ya tilasta musu mayar masa da kudaden da muka tura asusun gwamnati ta hannun mukarrabansa bayan an sa asun canza kudaden zuwa Dalar Amurka.

“Sun tabbatar da cewa ba su yi wa jihar Zamfara wani aiki ba amma an umarce su da su maida kudaden da aka tura musu, aka kuma bukaci dole su mayar da su dalar Amurka su mayar wa gwamanatin jihar ta hannun wasu kwamishinoni, musamman na kudi da kananan hukumomi,” in ji shi.