✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta janye umarnin tsare Shugaban EFCC

Kotu ta ce ta gano Shugaban EFCC bai yi watsi da umarninta ba

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da umarnin da ta bayar na tsare Shugaban Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) bisa laifin raina kotu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Chizoba Oji, ce ta dakatar da umarninta na kama shugaban na EFCC da kuma aike wa da shi gidan gyaran hali bayan ta saurari hanzarin da hukumar ta gabatar.

Ta ce kotun ta gano cewa Shugaban Hukumar EFCC bai raina umarninta ba, hasali ma ya bi umarnin na mayar wa Ojuawo motarsa da kuma Naira miliyan 40 da hukumar ta kwace.

Shugaban na EFCC ya yi hakan ne ta wasu wasiku da ya aika na cikin gida, yana ba da umarnin tabbatar da biyan Naira miliyan 40 da kotun ta yi umarni da kuma sakin motar.

A ranar Talata ne alkalin ta umarci Babban Sufetan ’Yan Sandan Najeriya ya kama shugaban hukumar saboda zargin raina kotu ta hanyar kin bin umarnin da ta bayar.