✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta ba da umarnin fitar da Sarki Bayero daga Fadar Nassarawa

Za mu soma yi wa Fadar Nassarawa kwaskwarima nan ba da jimawa ba.

Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga karamar fada ta Nassarawa da yake zaune a cikinta.

Gwamnatin ta bai wa kwamishinan ’yan sandan jihar wannan umarni tana mai cewa akwai kwaskwarima da za ta soma yi wa ginin fadar nan ba da jimawa ba.

Kwamishinan Shari’a kuma Lauyan Ƙoli na Jihar Kano, Barista Haruna Isa Dederi ne ya bayar da wannan sanarwar yayin wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis a Fadar Gwamnatin Kano.

Wannan dai na zuwa ne bayan hukuncin da wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar ta yanke a yau dangane da taƙaddamar Masarautar Kano.

Babbar Kotun Tarayyara ta ce dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya ce ba daidai bane gwamnan jihar Kano ya aiwatar da dokar soke masarautun saboda akwai umurnin kotun da aka bayar da ya dakatar da duk wani yunkuri na gwamnan Kano wajen aiwatar da sabuwar dokar da ta cire rawanin sarakuna biyar a jihar ta Kano.

Mai shari’a Liman ya ce “A don haka na bayar da umurnin cewa dukkan matakan da gwamnati ta ɗauka na soke su amma hakan bai shafi sabuwar dokar masarautu ba. Amma sun shafi matakan da gwamna ya dauka ciki har da sanya hannu a sabuwar doka da kuma sake nada Sanusi..

Kotun ta ce “An soke dukkan matakan da masu kare kai a shari’ar suka ɗauka, amma kuma hakan bai shafi dokar ba.”

“Waɗanda ke kare kansu a shari’ar na sane da umurnin kotun duk da cewa ba a aika musu da kofin umurnin ba. Amma sun gani a kafafen soshiyal midiya, a don haka ba daidai bane su kawar da kai”, in ji Alkali Liman.

Mai shari’a Liman ya mayar da wannan ƙara zuwa wata Kotun Tarayyar karkashin mai shari’a Amobeda Simon amma har sai an kammala sauraren karar da ɓangaren gwamnati suka ɗaukaka.

Wannan al’amari na dambarwar masarautar Kano, tana ci gaba da ɗaukar hankali inda jama’a ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.

A watan Mayun da ya gabata ne dai ’yan Majalisar Dokokin Kano suka yi ƙudirin dokar inda kuma ba tare da ɓata lokaci ba Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya mata hannu ta zama doka.

Bisa dokar ne gwamnan ya rushe sarakunan biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16, bayan da tsohon gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe shi a 2020.

To sai dai kuma a ranar 23 ga watan na Mayu ne ɗaya daga cikin masu naɗa sarkin Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi mai sarautar Sarkin Dawaki Babba ya ƙalubalanci dokar a Babbar Kotun Tarayyar da ke Kano, inda ya nemi alƙalin da ya ayyana dokar a matsayin haramtacciya.