Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta mayar da Kwamared Philip Shaibu kan kujerar Mataimakin Gwamnan Jihar Edo watanni uku bayan tsige shi.
Mai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ne ya yanke wannan hukuncin a zaman shari’ar yau Laraba, 17 ga watan Yuli, 2024.
- Yadda na tsere da daga hannun ’yan bindiga —Mai shayarwa
- Majalisar Dattawa ta tsige Sanata Ali Ndume
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Omotoso ya ce Majalisar Dokokin Jihar Edo ta saba wa tanade-tanaden doka wajen sauke mataimakin gwamnan.
Alƙalin ya bayyana cewa matakin tsige Shaibu ya saɓa wa tKundin Tsarin Mulkin Nijeriya.
Baya ga mayar da shi, kotun ta ba da umarni a biya shi albashi da alawus alawus ɗinsa tun daga lokacin da aka tsige shi.
Sai dai, Majalisar Dokokin Edo ta ɗaukaka ƙara kan hukunci da kotun ta yanke.
Majalisar ta kuma nemi a dakatar da aiwatar da hukuncin sai Kotun Ɗaukaka Kara ta yanke hukunci a shari’ar.
A ranar 8 ga watan Afrilu da ya gabata ne ’yan majalisar suka tsige Kwamared Shuaibu wanda ya sha fama da takun-saka tsakaninsa da Gwamna Godwin Obaseki.