Ci gaba da faduwar darajar Naira ya sa canjin Fam na kasar Birtaniya ya kai Naira 1,000 a kasuwar bayan fage a karshen mako.
Ana cike da fargabar cewa yayin da aka wayi garin Litinin a farkon makon nan, Dalar Amurka ita ma za ta kai Naira dubu daya ko fiye da haka.
- Canjin Naira: EFCC ta dana wa gwamnoni tarko —Bawa
- Majalisa ta yi sammacin Emefiele bayan canjin Dala ya kai N700
Farashin canjin bayan fage ba shi da amincewar Babban Bankin Najeriya (CBN), amma wani karin nauyi ne kan darajara Naira ne da kuma kara buda gibi tsakanin canjin gwamnati, da matsala ga harkokon kasuwanci.
A makon da ya wuce Hukumar EFCC ta kai samame wasu ofisoshi canjin kudi masu lasisi a Abuja da Legas da kuma Kano a kokarinrta na dakile faduwar darjar Naira amma hakan bai yiwu ba.
’Yan Najeriya da yawa sun nuna takaici da kaduwa da jin cewa canjin Fam daya ya koma N1,005 a shafukan sada zumunta a karshen mako.
“Yanzu Fam dubu daya ta koma Naira Milyan daya ke nan, lallai kasar nan mun shiga uku!” a cewar Salami Azeez wani a shafinsa na Twitter.
A kwanaki Daily Trust ta rawaito cewa, shirin gwamnati na sauya fasalin Naira da CBN ke yi ya sa mutane da yawa yin rubibin zuwa canza kudadensu zuwa na kasashen waje.