✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanariyar Saminaka ta lashe zaben kujerar Majalisar Dokokin Kaduna

Hukumar INEC, ta bayyana Zinariyar Saminaka, Hajiya Munira Suleiman Tanimu ta jam’iyyar APC, a matsayin wadda ta lashe zaben kujerar Majalisar Dokokin jihar Kaduna, ta…

Hukumar INEC, ta bayyana Zinariyar Saminaka, Hajiya Munira Suleiman Tanimu ta jam’iyyar APC, a matsayin wadda ta lashe zaben kujerar Majalisar Dokokin jihar Kaduna, ta Mazabar Lere ta Gabas da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, da aka gudanar a ranar Asabar nan da ta gabata.

Zaben Kano: APC tana gaban NNPP da kuri’a 1113

Da yake bayyana sakamakon zaben a garin Saminaka, babban Baturen zaben Farfesa Abdullahi Dalhatu, ya bayyana cewa Manira Suleiman Tanimu ta APC ta sami kuru’a 23,275. A yayin da Garba Emmanuel Bajimai na APGA ya sami kuru’a 1419 sai Muhammad Sunusi Sufwan na LP ya sami kuru’a 7158.
Ibrahim Muktar na NNPP ya sami kuru’a 2137. Sa’idu Hussaini na PDP ya sami kuru’a 22,964. Don haka Munira Suleiman Tanimu  APC ce ta lashe wannan zavb.