Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba.
Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba.
Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun 2031.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Obi ya bayyana hakan a yayin amsa tambayoyin magoya bayansa wata hira ta kai tsaye da aka yi da shi a shafin X a ranar Lahadi.
Obi ya musanta kulla yarjejeniyar tsayawa takara a karkashin tikiti daya da tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar.
Haka kuma, Obi ya ce duk wata haɗaka da za a yi wadda ba ta da kudirin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihohin Benuwe da Zamfara…da kuma bunkasa tattalin arzikin Nijeriya, to kuwa babu shi babu ita.
Kazalika, Obi ya ce yana goyon bayan tsarin da zai bayar da damar a rika karɓa-karɓar mulki a tsakanin Kudu da Arewacin Nijeriya.