Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi ya ce zai yi sulhu da haramtacciyar kungiyar IPOB mai neman ballewa daga Najeriya da sauransu, idan ya ci zabe a 2023.
Peter ya bayyana cewa idan ya ci zabe, kamun ludayin gwamnatinsa zai kasance da tattauna da duk wata kungiya ko bangarori masu korafi ko matsala da gwamanti domin yin sulhu da samun daidaito.
- Dalibai 3,000 sun sa hannu kan bukatar ABU ta koma bakin aiki
- Ministar Kudi da Akanta-Janar na manakisa ga yaki da rashawa —Majalisa
Ya sanar da haka ne a hirar da aka yi da shi kan sha’anin tsaron Najeriya a hedikwatar Rukunin Kamfanin Yada Labarai na Media Trust masu jaridar Daily Trust da Aminiy da kuma Trust TV a Abuja.
A cewarsa, “Na sha fada, Najeriya ba ta kai kasar Brazil yawan masu korfai ba; Idan kuna so zan bayyana muku kasashen da a baya suka yi fama daga irin wadannan korafe-korafe, kama da Brazil zuwa Meziko da sauransu.
“A yankin Kudu maso Gabas, sulhu zan yi da su, mu tattauna tun da dimokuradiyya ce kuma a dimokurasiyya za a iya shugabanci ta hanyar sulhu.
“Idan da wanda bai ji dadin abin da aka yi ba ba, sai ka kira shi ku zauna ku tattauan.
“Ko a gidana matata da ’ya’yana sukan yi korafi. Duk wanda ya ce tun da suke tare da matarsa ba su taba samun sabani ba, to sai dai idan ba aure suke yi ba. Akan samu sabani, sannan a sasanta — wannan shi ne korafi.”
IPOB haramtacciyar kungiya ce mai rajin ballewa daga Najeriya da kuma kafa kasar Biyafara — wadda za ta kunshi Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu na Najeriya.
Barazanar IPOB
Hare-haren kungiyar sun zama babbar barazanar tsaro a yankunan biyu, inda baya ga kashe-kashe da kone-kone, kungiyar kan hana mutanen yankunan fita daga gidajensu domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
A shekarar 2017 kotu ta ayyana kungiyar a matsayin ’yar ta’adda bayan Gwamnatin Tarayya ta maka shugaban kungiyar, Nnamdi Kanu a kotu kan ayyukan ta’addanci.
Ana kuma zargin kungiyar da kashe jami’an tsaro da ’yan siyasa da sarakuna har ma da daidaikun ’yan Najeriya.
Ana kuma zargin ’ya’yanta da kai hare-hare kan gine-gine da cibiyoyin gwamnati , kamar ofisoshin ’yan sanda da na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), a yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.
A 2012 Nnamdi Kanu, dan Najeriya mazaunin Birtaniya ya kafa kungiyar; Kano ya yi kaurin suna wajen neman ballewa daga Nejeriya domin kafa kasar Biyafra.
Barazanar tsaro a Arewa
Baya ga IPOB a yankun Kudu, shekara 13 ke nan yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na fama da matsalar ta’addancin Boko Haram/ISWAP.
Rikicin ta’addancin Boko Haram/ISWAP, masu ikirarin nema kafa daular Islama ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 100,000 tare da raba sama da miliyan biyu da gidajensu, baya ga wadadna suka samu raunuka.
Baya ga wannan ayyukan kungiyar sun kuma hana ci gaba da ayyukan hako arzikin mai da aka gano a yankin na Arewa maso Gabas.
A shekarun baya-bayan nan kuma, ayyukan masu garkuwa da mutane domin karbar kudaden fasa — wadanda aka fi sani da ’yan bindiga — sun yi kamari a yankin Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta Tsakiya.
Barazanar kasar Yarabawa zalla
A yankin Kudu maso Yammaci kuma, akwai matsalar masu fafutukar ballewa domin kafa kasar Oduduwa, ta Yarabawa zalla.
Yunkurin, wanda Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ke jagoranta, ya haifar da hare-hare musamman kan al’ummar Fulani a yankin Yarbawa.
Tafiyar ta Igboho na zargin Fulani a yankin Yarabawa da zama ’yan share-wuri-zauna da ke mamaye yankin suke kuma kai hare-hare a kan ’yan kasa, zargin da Fulanin suka karyata.
Baya ga wadannan, akwai rikice-rikicen kabilance, kama daga taskanin manoma da makiyaya, zuwa tsakanin kabilu marasa ga maciji da sauransu a sassan Najeriya.
Yadda salon mulki na zai kasanci —Peter Obi
Amma da yake magana kan yadda zai shawo kan matsalar, tsohon Gwamnan Anambran ya ce, zai yi kokarin yin sulhu da kowane bangre domin samun damar gudanar da mulkin Najeriya yadda ya kamata.
“Zan saurari kowa, kuma zan ziyarci kowane bangare; Muna kasa mai fadin gaske a Arewa, wadda idan aka yi amfani da ita, aka noma yadda ya kamata, za ta kawo kyakkyawan sauyi a Najeriya.
“Gwargwadon yadda gwamnatina take rage talauci, gwargwadon yadda za a samu raguwa korafe-korafe da aikata manyan laifuka.
“Duk wadannan abubuwa da ke faruwa yanzu ba komai ba ne face abin da gazawar gwamnatoci na tsawon lokaci ta haifar; abin da nake so shi ne a dauke ni a matsayin mutumin da zai kawo sauyi a kasar nan, Najeriya,” in ji shi.
Matsayin ta’addancin IPOB
Da aka tambaye shi game da matsayinsa kan ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci, tsohon gwamnan Anambaran ya ce bakinsa da goro.
“Ba na son yin magana a kan wannan; Na riga na bayyana cewa zan yi sulhu da kowa, ko da wane suka ake kiran ka, zan neme ka mu tattauna.
“Ban so a yi wa mutane kamar yadda aka yi a lokacin tarzomar EndSARS; zan ba da hakuri. Dole ya zama muna yin yafiya da nuna kauna a matsayin al’ummar kasa guda, wannan shi ne tsarin dimokuradiyya.
“Zan tattauna da mutanen Arewa da duk sauran yankunnan kasar nan mu zama uwa daya, uba daya.
“Ina in ga ’yan Najeriya suna alfahari da kasancewarsu ’yan kasar; Sabanin yanzu da muke da Najeriya amma ba ma son a ce mana ’yan Najeriya. Wannan shi ne abin da nake son canzawa.”
Daga: Sagir Kano Saleh, Ismail Mudashir & Fidelis Mac-Leva