✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan yi sauye-sauye a kwamishinonin Kano — Abba

Na naɗa kwamishinonin ne bisa la’akari da ƙwarewa da cancanta da kuma neman shawarwari.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana aniyarsa ta aiwatar da sauye-sauye a Majalisar Zartarwas jihar yana mai cewa zai sauke duk wani kwamashinansa da aka gano ba shi da himma a aikinsa nan gaba kaɗan.

Gwamnan ya yi wannan tsokaci ne yayin wata hirar da ya yi da manema labarai a fadar gwamnatin jihar a ranar Laraba da daddare.

A cewarsa, babu ko ɗaya daga cikin kwamishinonin da ya nemi kujerar gabanin naɗinsu, inda ya ce ya naɗa su ne bisa la’akari da ƙwarewa da cancanta da kuma neman shawarwari.

Kazalika, Abba ya ce abin da har yanzu yake tsammani daga kwamishinonin shi ne kiyaye umarni da yi wa gwamnatinsa biyayya da jam’iyyar NNPP da kuma ƙungiyar Kwankwasiyya kan duk wani aiki da zai kawo ci gaban Jihar Kano.

Haka kuma, wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature ya fitar a ranar Juma’a, ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamatin da ke duba ƙwazon kwamashinonin.

“Nan gaba kaɗan al’umma za su ji matakin da gwamnatin za ta ɗauka,” in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa “gwamnan ya ce rahoton ma ba zai yi wani amfani ba yanzu saboda tsawon shekara ɗaya da rabi da ya yi yana aiki tare da su ya ba shi damar gane himmarsu ciki da baya, saboda haka da kansa zai yanke hukuncin.”