✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da Sallah

Sarkin bai cika duk tsare-tsaren da al’ada ta tanada ba na gudanar da Hawan Sallah.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar.

Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara.

Sai dai a sakamakon haramcin gudanar da haye-hayen sallah da rundunar ’yan sandan jihar ta yi, Sarkin bai cika duk tsare-tsaren da al’ada ta tanada ba na gudanar da Hawan Sallah.

Aminiya ta ruwaito cewa, Sarkin wanda ya yi ƙoƙarin kawar da idon jama’a, ya bi ta wasu hanyoyin da ba su aka saba bi wajen kai wa gwamna ziyara a yayin gudanar da hawa cikakke.

Haka kuma, Sarkin ya yi amfani da jerin gwanon motoci ƙalilan maimaiko hawa dawakai

Sai dai an tsananta tsaro a duk hanyoyin da Sarkin ya bi tun daga Fadar Sarki ta Gidan Ƙofar har zuwa Gidan Gwamnatin Kano.