✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan yi rusau a Abuja — Wike

Wike ya ce duk wanda ya yi gini a wuraren da gwamnatin ta hana sai ya rushe su.

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi barazanar fara rushe gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba a Babban Birnin Tarayyar.

Ministan ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko a ofishin Hukumar Babban Birnin Tarayyar da ke Abuja a ranar Litinin.

Yana cikin ministoci 45 da shugaba Bola Tinubu ya rantsar da su yau Litinin a Fadar Shugaban Kasa.

Wike ya sha alwashin yin watsi da tsarin da ke kawo cikas ga gine-ginen Abuja.

“Mutanen da ke karkatar da tsarin Abuja, muna sane da ku… a duk inda kuke.

“Me ake yi da tarkace a Abuja? Don haka dole ne mu zauna mu duba hanyoyi daban-daban na zubar da shara.

“Duk wadancan mutanen da suke karkatar da tsarin Abuja, to wallahi idan ka san ka yi gini a inda bai kamata ba, kasan cewa ko kai minista ne ko ambasada sai mun rushe ginin.

“Idan ka san ka yi gini inda bai kamata ba dole ne a rushe shi.

“Wadanda suka yi gini a wuraren da aka ware don shuka, ina tausaya muku.

“Don haka, idan kun san kuna da wani wanda ke da hannu, duk wanda ya mallaki wuraren shakatawa zuwa gidajen cin abinci, ba za mu yarda da hakan ba.

“Yi hakuri, idan mahaifinka ko mahaifiyarka ne ya aikata hakan ku yi hakuri ba abin da zan iya sai an rushe wajen.

“Lokacin neman filaye ya kare. Zan soke duk inda aka bayar. Za mu kwace filayenmu. Kada ku biya kudin hayarku. Rashin biyan kudin hayar kasa saba alkawari ne.

“Abuja ma tana bukatar kudi. Tushen kudaden shiga ya hada da hayar kasa. Don haka, idan ba ku biya ba, ba zan gaji da soke lasisinku ba.”