Sergio Busquets ya tabbatar da zai bar Barcelona a karshen kakar nan, bayan shekara 18 yana Camp Nou.
Tsohon dan kwallon tawagar Sifaniya, mai taka leda daga tsakiya ya yi wa Barca karawa 718 – shi ne na uku a yawan buga wasa a kungiyar.
- EFCC ta kama tsohon Ministan Buhari na Lantarki
- Buhari zai karbo bashin Dala miliyan 800 daga Bankin Duniya
Dan kwallon ya lashe kyautuka da yawa a Barca ciki har da daukar La Liga takwas da Copa del Rey bakwai da Spanish Super Cup bakwai da Champions League uku.
Busquets ya koma Barca a 2005 a matakin matashin dan kwallo daga nan har ya koma babbar kungiyar, inda ya fara wasa karkashin Pep Guardiola a 2008 a gasar La Liga a karawa da Racing Santander.
Dan kwallon wanda ya lashe European Super Cups uku a Barca da Fifa Club World Cups uku zai dauki La Liga na tara a kakar nan.
Kungiyar da Xavi ke jan ragama tana matakin farko a kan teburin La Liga da tazarar maki 13, kuma saura wasanni biyar a kammala kakar bana.
A kaka 15 da ya yi yana buga wa babbar kungiyar Barcelona ya ci kwallo 18 ya kuma bayar da 40 aka zura a raga.
Busquets ya yi ritaya daga buga wa tawagar Sifaniyar tamaula a cikin watan Disamba, bayan da ya lashe kofin duniya a 2010 da European Cup a 2012.