Shugaban Amurka, Joe Biden, ya yi wa sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu alkawarin yin aiki tare wajen bunkasa tattalin arziki.
Ya kuma sha alwashin hada kai da Tinubu wajen inganta harkokin tsaro a Najeriya da dai sauran muhimman abubuwan da gwamnatinsa ke da su.
- NAJERIYA A YAU: Shin Da Gaske Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur?
- An kashe ’yan ta’addan ISWAP 3 a Borno
Biden ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, yayin da yake taya Tinubu murna a ranar Litinin.
Shugaban alkalan Najeriya, Kayode Ariwoola, ne ya rantsar da shugaba Tinubu tare da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a ranar Litinin.
Shugaban na Amurka ya sake nanata shirin gwamnatinsa na yin aiki tare da Tinubu “don karfafa dangantaka tsakanin Amurka da Najeriya.”
Biden ya ce, “A madadin jama’ar kasar Amurka, ina mika sakon gaisuwa ga gwamnati da al’ummar Najeriya yayin da suke kaddamar da sabon shugaban kasa.
“Ina fatan ci gaba da yin aiki tare da Shugaba Tinubu don tallafa wa cigaban tattalin arziki da inganta tsaro da kuma mutunta hakkin dan Adam.”
Ya kuma bayyana fatansa game da kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu, inda ya yi nuni da cewa, Amurka za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da kasa mafi yawan jama’a a Afirka.
Biden ya ce, “A matsayinta na babbar kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya da karfin tattalin arziki a Afirka, nasarar Najeriya ita ce nasarar duniya.
“Zababbun shugabanni suna bin al’ummarsu da su nuna cewa dimokradiyya za ta iya biyan bukatunsu.
“Kuma Amurka za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da Najeriya, a matsayin kawa kuma abokiyar aiki, don samar da kyakkyawar makoma cikin zaman lafiya da wadata ga duniyarmu.”
Shugaban kasar Amurka ya aike da tawaga da ta halarci bikin rantsar da Tinubu.