✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan tsaya takarar Shugaban Kasa a zaben 2023 – Tambuwal

Gwamnan ya ce zai tsaya takarar ne a tutar jam’iyyar PDP.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ce zai tsaya takarar Shugaban Kasa a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Ya bayyana matsayin nasa ne ranar Litinin a Sakkwato, inda ya ce shi ne ya fi cancanta da ya ja ragamar kasar a badi.

Gwamna Tambuwal dai ya taba neman tsayawa takarar gabanin zaben shekarar 2019, amma ya sha kaye a hannun tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, yayin zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP.

Ya ce a wannan karon ma, zai sake neman takarar ne a karkashin tutar jam’iyyar ta PDP.

Tambuwal dai ya taba zama Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya tsakanin shekarar 2011 da 2015.