✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan tsaya takarar shugaban Chadi — Mahamat Deby

Ni ne ɗan takarar shugaban ƙasa na gamayyar jam’iyyun United Chad Coalition.

Shugaban mulkin sojin Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen da za a yi a watan Mayu mai zuwa.

Mahamat Idriss Deby, ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi ranar Asabar a N’Djamena, babban birnin ƙasar.

A jawabin da ya yi, ya ce “Ni, Mahamat Idriss Deby Itno, ne ɗan takarar shugaban ƙasa na gamayyar jam’iyyun United Chad Coalition a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024.”

Hukumar zaɓen ƙasar ta ce za a gudanar da zagayen farko na zaɓen a ranar 6 ga watan Mayu mai zuwa.

A tsakiyar watan Janairun da ya gabata ne jam’iyyar Patriotic Salvation Movement (MPS) ta ayyana Mahamat Deby Itno a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa.

Deby Itno ya hau kan mulki ne a shekarar 2021 bayan mahaifinsa Idriss Deby Itno, wanda ya kwashe kusan shekara talatin a kan mulki, ya mutu a fagen yaƙi yayin fafatawa da wasu ƴan tawayen ƙasar.