✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan tabbatar an hukunta wanda ya yi batanci ga Annabi – Tambuwal

Ko a ranar Alhamis sai da aka gudanar da zanga-zanga kan hakan a Fadar Sarkin Musulmi.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya sha alwashin cewa gwamnatin Jihar za ta tabbatar an hukunta matashin da ya yi batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W) a Jihar.

Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Alhaji Isah Bajini Galadanci ne ya ba da tabbacin a madadin Gwamnan yayin wani taron manema labarai a Sakkwato ranar Juma’a.

Ya ce gwamnan ya yi Allah-wadai da lamarin tare da tabbatar wa da al’ummar Jihar cewa gwamnati za ta tabbatar an hukunta wanda ya aikata laifin.

“Gwamna ya yi tir da lamarin batanci da Annabi (S.A.W) kuma ya nuna damuwa tare da la’antar lamarin, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci ci gaba da aikata hakan ba.

“Duk wanda ya zagi annabin Rahama (S.A.W) ko wani Annabi ba za zura sa masa ido ba. Jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi domin daukar mataki kan lamarin, kuma za a gurfanar da shi gaban kotu, matukar aka same shi da laifi za a hukunta shi daidai laifin nasa,” a cewarsa.

Kwamishinan ya kuma ja hankalin mutane da su guji siyasantar da lamarin kuma su hada hannu domin ciyar da Jihar gaba.

Ko a ranar Alhamis dai sai da wasu mutane suka gudanar da zanga-zangar nuna Allah-wadai a Fadar Sarkin Musulmi da ke birnin na Sakkwato saboda nuna rashin jindadinsu kan lamarin tare da neman a hukunta wanda ya aikata.