✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan soke wasu tsare-tsaren El-rufa’i idan na zama Gwamnan Kaduna – Ashiru

Ya ce matukar aka zabe shi, zai sauya abubuwa da dama a Jihar

Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a jam’iyyar PDP, Isah Ashiru Kudan, ya sha alwashin soke wasu tsare-tsaren gwamnatin APC muddin ’yan Jihar suka zabe shi a matsayin gwamna a 2023.

Ashiru ya bayyana haka ne cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun Daraktan Hulda da Jama’a na Kungiyar Yakin Neman Zabensa, Yakubu Lere El-Saed.

Haka nan, dan takarar ya jajanta wa Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT) reshen Jihar, dangane da korar mambobinta sama da 2,000 da gwamnatin Jihar ta yi.

Ya ce zai sauya wasu dokoki da tsare-tsaren da gwamnatin APC ta shimfida a fannin ilimin Jihar  muddin ’yan jihar suka ba shi damar da yake bukata.

A cikin sanarwar tasa, Ashiru ya kalubalanci dan takarar Gwamna na APC a Jihar, Sanata Uba Sani, ya fayyace matsayarsa dangane da korar malaman da gwamnatin Jihar ta yi kwanan nan, da kuma shirin da take da shi na rushe Kasuwar Gwari da ke Rigasa da kuma kasuwar da ta rushe a yankin Karamar Hukumar Saminaka a Jihar.