Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi Alhaji Haliru Abubakar Gwandu ya ce zai sa kafar wando daya da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a dukkan kananan hukumomin jihar 20 ganin yadda matsalar ta zamo ruwan dare a kasar nan.
Alhaji Halliru Gwandu ya bayyana haka ne lokacin da ya kira taron masu ruwa-da-tsaki a bangaren tsaro da ya hada da kungiyar samar da tsaro ta Danga da ’yan sintiri da Alhaji danladi Gamji ke shugabanta.
Kwamishina daga bisani an gayyaci shugabannin kananan hukumomin Ningi da Ganjuwa daToro da Darazo da sarakunan gargajiya na yankin domin ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar garkuwa da mutane a yankunansu.
“Babban abin takaici shi ne mafi yawan wadanda ’yan sanda suke kamawa Fulani ne, don haka daga yanzu duk wanda rundunar ta kama tabbas zai dandana kudarsa,” inji shi.
Kkwamishina Gwandu ya ce babbar matsalar da take addabi jihar ita ce ta masu garkuwa da mutane musamman a karamar Hukumar Toro inda masu garkuwa da mutanen suke cin karensu babu babbaka, ya ce yanzu ’yan sanda sun tashi tsaye domin ganin bayansu.
Da yake zantawa da Aminiya a ofishin Kwamishinan, Mataimakin Shugaban kungiyar Kyautata Dangantaka a Tsakanin ’Yan sanda da Jama’a (PCRC) na jihohin Arewa 19, Alhaji Sunusi Maijama’a ya ce za su ba da duk gudunmawar da ta kamata domin magance matsalar masu garkuwa da mutane a jihar.
Alhaji Sunusi Maijama’a ya ce kungiyar za ta ci gaba da taimaka wa ’yan sanda ta yadda za a samu nasarar kawar da masu aikata miyagun laifuffuka a tsakanin jama’a.
Zan mu sa kafar wando daya da masu garkuwa da mutane a Bauchi – Kwamishina
Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi Alhaji Haliru Abubakar Gwandu ya ce zai sa kafar wando daya da masu garkuwa da mutane domin neman kudin…