✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan mika dokar yanke hannun masu cin hanci – Smart Adeyemi

Ya ce ba za mu tsaya suna kallo wadansu na cinye kudin gwamnati ba.

Shugaban Kwamitin Harkokin Sufurin Jiragen Sama a Majalisar Dattawa, Sanata Smart Adeyemi, ya ce ya kammala shirye-shirye don gabatar da wani kudirin doka gaban majalisar don yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.

Sanata Adeyemi ya ce, kudirin dokar zai kunshi tsarin Shari’ar Musulunci da na Kirista kuma idan ya tabbata, zai ba da damar yanke hannu masu cin hanci da satar dukiyar jama’a ba tare da la’akari da matsayinsu ba.

A hirar da ya yi da BBC, Sanatan ya ce, a Najeriya idan aka kama mutum ya saci kudin gwamnati ba a yi masa hukuncin da ya dace, sai a ja shekaru a na shari’a daga bisani maganar ta sha ruwa.

Ya ce, “Shari’ar da nake so kuma zan gabatar da kuduri a kanta a gaban majalisarmu ita ce duk wanda ya ci kudn gwamnati aka kuma kama shi to a hukunta shi, ma’ana ko alkali ya kwatanta ya ga idan ya kamata a yanke wa mutum hannu sai a yanke, idan bai kai haka ba to sai a tanadi hukunci na kai mutum gona ya yi ta aiki a can.”

Sanatan ya ce “Idan ana irin wannan hukunci na aiki mai wahala ko yanke hannun masu satar kudin gwamnati, mutane za su shiga taitayinsu.”

Ya ce idan ba a sanya dokar da za ta sa mutane su ji tsoro cin kudin gwamnati ba, to ba za a taba samun wani ci gaba a Najeriya ba.

“Amma idan aka sa dokar da mutum zai san ko a yanke masa hannu ko ya shafe shekara biyu yana noma idan ya saci kudin gwamnati, to wallahi mutane za su daina,” inji shi.

Sanata Adeyemi ya ce irin wannan hukunci ba a shari’ar Musulunci kawai ake yin sa ba, akwai shi a cikin Baibul.

Ya ce ba za su tsaya suna kallo wadansu na cinye kudin gwamnati ba, saboda da irin wadannan kudade ne ake gina ababen more rayuwa kamar asibitoci da tituna da makarantu da sauransu ga jama’a.

Sanatan ya ce, “Sai mutum ya sace biliyoyin kudin gwamnati, to me ya rage gara a hukunta mutum a dan rage masa hannunsa ma’ana a yanke masa hannu ta yadda idan wani ya gani ba zai kwatanta ba.

Idan Allah Ya yarda kafin karshen bana nake son gabatar da kudirin dokar gaban majalisarmu, domin idan ana so a samu ci gaba a kasa dole a yi doka a kan masu cinye kudin gwamnati.

Don haka ya rage ruwan ’yan majalisarmu su yi abin da ya dace kan wannan kudiri, don ni na fita da zarar na gabatar,” inji Adeyemi.

%d bloggers like this: