Shugaban Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), Ola Olukayode, ya bayyana cewa yanzu hukumar tana yaƙi da cin hanci daga tushe ne, ta hanyar daƙile shi daga ma’aikatu da sauran hukumomi.
Ya bayyana haka ne a Kano, yayin wani taro da aka gudanar a cibiyar nazarin dimokuraɗiyyar ta Aminu Kano (Mambayya).
- An kama mai motar da aka samu AK-47 a ciki
- Mutane na komawa gida bayan janyejwar ambaliyar Maiduguri
Taron wanda Cibiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam da Wayar da Kai (CHRICED), ta shirya mai taken: “Fayyace Gaskiya, Taimakon ’Yan Ƙasa wajen Yaƙi da Cin Hanci a Najeriya.”
Olukayode, ya ce “Abin da muke yi shi ne shiga ma’aikatu, sassa da hukumomi, muna sanya ido kan tsarin kwangila domin tabbatar da cewa ana bin doka. Yawancin cin hanci yana faruwa ne ta hanyar kwangila da tsarin saye da sayarwa.
“Idan ka yi wa wannan tsari gyara, za a samu ingantaccen aikin gudanarwa. Matsalar ita ce, mutane na karbar kuɗi amma ba sa kammala aikin da aka ba su, kuma wannan yana haifar da cin hanci.”
Ya ƙara da cewa, “Tun daga lokacin da aka fitar da kuɗi, za mu fara sanya ido kan yadda ake gudanar da aiki. Idan an samu giɓi a tsarin kwangilar, za mu sanar da cewa su gyara don tabbatar da gaskiya.
“Lokacin da aka bayar da aikin, za mu duba ko an yi abin da aka fitar da kuɗin domin sa. Wannan ita ce hanya mafi tsari a yaƙi da cin hanci kuma ita ce abin da muke shirin yi.”
Sai dai ya ce wannan ba zai kawar da cin hanci gaba daya a Najeriya ba, amma ya ce, “Idan ka yi wa wannan tsari zubi mai kyau, za a samu raguwar cin hanci sosai.”
A nasa ɓangaren, Daraktan Cibiyar CHRICED, Dokta Ibrahim Zikrullah, ya bayyana cewa cin hanci yana shafar kowane ɓangare na ci gaban ƙasa.
Ya ce yana a rage amincewa da hukumomin gwamnati, sannan yana hana a cimma gagarumin ci gaba.
Ya jaddada buƙatar samar da tsarin yin gaskiya da amana domin tabbatar da cewa an yi amfani da albarkatun ƙasa wajen amfanar da al’umma.
Farfesa Muhammad Sani Gumel, Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, ta Kano (Fannin Koyarwa), wanda ya shugabanci taron, ya ce taron ya zo a kan gaɓa.
Ya ce taron ya yi daidai a yanzu da ake yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar nan karkashin kulawar hukumomin yaƙi da cin hanci.