✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan kori ’yan kasuwar da ke tsawwala farashin kayan abinci a masarautata — Ooni na Ife

Muna maraba da wannan mataki— Hausawa

Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi ya bayar da umarnin korar duk ɗan kasuwar da aka same shi da tauye mudu ko tsawwala farashin kayan abinci a kasuwannin da ke masarautar Ile-Ife a Jihar Osun.

Kuma Sarkin ya ce za a rufe duk kasuwar da aka gano irin waɗannan ’yan kasuwa suna ƙayyade farashin kayan abinci da sunan haramtattun ƙungiyoyin da suke kafawa.

Oba Enitan Ogunwusi ya bayar da wannan umarni ne a saƙon da ya aika ta hannun manyan hakimai 16 don isar da saƙon ga ’yan kasuwa ta hanyar ziyartar kasuwanni daban­daban a Masarautar Ife.

Da suke isar da saƙon Sarki a kasuwannin da suka ziyarta, hakiman da suka samu rakiyar iyayen kasuwa maza da mata ‘Babaloja’ da ‘Iyaloja’ sun yi amfani da lasifika wajen yin yekuwar.

Sun bayyana cewa “Mai martaba Ooni na Ife ya aiko mu shaida muku cewa daga yanzu Fadar Sarki za ta ɗauki matakan ladabtar da dukkan ’yan Kasuwar da aka same su da laifin kafa haramtattun ƙungiyoyi da ake amfani da su wajen ƙayyade farashin kayan abinci da hakan ke haifar da tsadar kayan abinci ga mabuƙata.”

Yekuwar ta ce daga yanzu an soke aikin waɗannan ƙungiyoyi kuma kowane ɗan kasuwa na da ikon sayar da kayan abinci a kasuwanni yadda yake so.

“Fadar Sarki za ta ladabtar da dukkan masu tauye mudu wato ‘kongo’ daga gwangwani 10 zuwa 7 na nau’in kayan abinci da tsayar da farashin kayan miya a kan naira 500,” in ji yekuwar da ta ce daga yanzu irin wannan kayan miya kada farashinsu ya wuce Naira 200 zuwa 300.

Da yake yi wa Aminiya ƙarin haske Sarkin Samarin Ile-Ife Alhaji Ahmed S. Salihu wanda ke riƙe da sarautar Otun Babaloja na Kasuwar Waasin­ Ajoda a Ile-Ife ya ce al’ummar Hausawa sun yi maraba da wannan mataki da Ooni na Ife ya ɗauka domin tsame talakawa daga ƙuncin rayuwa.

Ya ce al’ummar Hausawa za su yi duk abin da za su iya  wajen ganin sun bayar da gudunmawarsu ga wannan sabon matakin da Sarkin Ile­Ife ya ɗaukar wanda ya zo a kan lokaci.

Ya yi kira ga Hausawa masu hada-hadar kasuwanci a Masarautar Ife su tabbatar da cewa sun yi aiki da yekuwar Sarkin.