Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce zai koma gona gadan-gadan da zarar wa’adin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kare a 2023.
Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar Manoma ta Kasa (AFAN), reshen Jihar Edo a ofishinsa.
- Dan NYSC ya dauki nauyin karatun marainiya da kudin alawus dinsa
- Zan yi amfani da fasahar zamani wajen magance matsalar tsaro — Saraki
A cewarsa, “Idan wa’adin gwamnatinmu ya kare a 2023, da yardar Allah ina da shirin komawa aikin jarida ka’in da na’in da kuma gona. Allah Ya taimaka mana Amin.
“Abin alfahari ne sosai lokacin da aka shaida min cewa za ku ziyarce ni don nada ni a matsayin uban kungiya.
“Na yi mamaki sosai sannan na tambayi kaina, ta yaya suka san ina da shirin komawa gona? Kamar suna duba?,” kamar yadda Femi Adesina ya wallafa.
Kakakin Shugaban Kasar dai ya yi aiki a gidajen jarida Vanguard da kuma National Concord, da kuma The Sun, har zuwa shekarar 2015 lokacin da ya ajiye matsayi Babban Editanta don fara aiki a gwamnatin Buhari.