✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan kayar da Zulum cikin sauki —’Yar takarar gwamna

Fatima Abubakar, ta kasance mace daya tilo da za ta fafata da 'yan takara 11 a zabe mai zuwa.

‘Yar takarar Gwamnan Jihar Borno a jam’iyyar ADC, Hajiya Fatima Abubakar, ta ce tana da kwarin gwiwar kayar da Gwamna Umara Zulum tare da lashe zaben gwamnan da za a gudanar a watan Maris, 2023.

Zan kayar da Zulum cikin sauki —’Yar takarar gwamna

Fatima, ita ce mace daya tilo da ta tsaya takara gwamna a jihar.

Ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Maiduguri cewa, salin alin za ta tika Zulum da kasa yayin da a ranar Laraba ta fara yakin neman zabenta gida-gida don neman goyon bayan jama’ar jihar.

Ta ce tana kara samun goyon baya da farin jini a wajen jama’ar jihar, inda ta ce tana kan hanyar lashe zaben da ke tafe.

“Ina kara samun farin jini tare da karin magoya baya, musamman matasa da matan da suka yi imani da zan kawo sauyi mai inganci a rayuwarsu.

“Ina so na yi kira ga mata da matasa da muke tuntubar juna, su ma su isar da sakona ga wasu kan bukatar a gwada mata a wannan takara don samun canji,” in ji ta.

Kazalika ta musanta rade-radin da ake yi na cewar ta janye daga takararta saboda ba a ganin hotunan yakin neman zabenta a allunan talla.

“Muna kan shirye-shiryen gudanar da gangami na musamman,” in ji Fatima.

A yayin da ta yi kira da a gudanar da yakin neman zabe cikin lumana, ta bukaci sauran ‘yan takara da su rika yin kamfe bisa ka’ida tare da mutunta juna a tsakaninsu da abokan hamayyarsu.

“Ya kamata mu yi aiki don inganta Borno ba don son kanmu ba, kuma ya kamata mu mutunta zabin mutane,” in ji ta.

Aminiya ta ruwaito cewa mata 16 ne kawai suke yunkurin neman mukamai daban-daban cikin ’yan takara 280 da za su fafata a zaben 2023 a Borno.

Fatima za ta kara da ‘yan takara 11 a zaben gwamnan jihar a ranar 11 ga Maris, 2023.