✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan kawo karshen rikicin Fulani da Makiyaya a Najeriya — Yariman Bakura

Fulani ’yan uwana ne don sunan da ake kiran Kakana Amadu Bahillace.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima, ya ce zai iya bakin kokarinsa wajen kawo karshen rikicin Fulani da Makiyaya a fadin kasar nan.

A karshen wannan mako ne Tsohon gwamnan ya bayyana haka yayin wani taro da Kungiyar FulbeYSO ta gamayyar kungiyoyin Fulani makiyaya magoya bayan takararsa ta Shugaban Kasa a zaben 2023 da suka fito daga Jihohin kasar nan 36 da Birnin Tarayya Abuja suka shirya masa.

Da yake gabatar da jawabin nasa yayin taron wanda aka gudanar a babban dakin taro na Otel din Jimson da ke Mararraba a Jihar Nasarawa, Sanata Yarima ya ce: “Fulani ’yan uwana ne kuma ni na fito daga cikinsu don sunan da ake kiran Kakana Amadu Bahillace.

“Ina mai tabbatar muku cewa zan yi iya bakin kokari na wajen kyautata rayuwar Fulani tare da maido da shanun Fulani Makiyaya a duk inda suke cikin kasar nan.

“Zan kawo Karshen rikice-rikice da ake samu da matsalolin da suka dabaibaye al’ummar Fulani da Makiyaya a Kasar nan.

“Sannan za mu bai wa Fulani damar fitar da wakilinsu guda da zamu nada a matsayin Minista kuma wakili a Majalisar Zartarwa ta Najeriya.

“Babban abun da yake damun jama’ar kasar nan shi ne rashin tsaro da karancin abun yi.

“Za mu iya bakin kokarinmu mu dora kan kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi na samar da tsaro da ayyukan yi ga matasa da farfado da masana’antunmu.”

A nasa Jawabin a wajen taron, Sanata Abdullahi Bala Adamu, ya ce Fulani suna da gudunmawa da rawar da za su taka a kasar nan wajen kawo sauyi, saboda ba kashin yarwa bane su kuma yanzu haka akwai kimanin kasashe shida a duniya da su ke rike da shugabancinsu.

Sanata Adamu, ya yi kiran da a rika yi wa Fulani adalci bisa la’akari da yadda a yanzu haka ake bata musu suna da darajar da suke da ita a idon duniya.

Ya ce ana yi wa Fulani yarfe na rashin son zaman lafiya da yi musu kudin goro da sunan masu satar mutane da jingina musu sauran ayyukan ta’addanci da ake yi a kasar nan.

Shugabannin kungiyoyin da suka fito daga yankunan Kudu da Arewacin Kasar na Jihohi 36 da Abuja, sun ce suna tare da tafiyar Yarima a shekarar 2023 kuma za su mara masa baya saboda shi ne nasu kuma shi suka sani saboda suna sa ran samun adalci daga gare shi tunda su ganau ne kan haka lokacin da yake gwamna a Jihar Zamfara.

Taron ya samu halartar Shugabannin Fulani da masu rike da sarautun gargajiya da ‘yan siyasa da shugabannin kungiyoyi da daruruwan mata da matasa.